Friday, 11 October 2024

kason masu rabon gado

Assalamu alaikum. Raba gado da "Fatwa" hukuncinsu daya ne. Bai kamata a yi tsada ba [AR-RAWDHATUN NADIYYA; 3/224, AL-MAWSU'ATUL FIQHIYYATIL KUWAITIYYA; 32/42]
Sheikh Abdurrazakyahayahaifan.
***********
Assalamu alaikum,
Allah ya taimake Malam.
 Don Allah kaso nawa ya kamata ko ya wajaba a cirewa malaman da suka yi rabon gaado daga dukiyar marayu?
 Wassalam
 Abdu Bello Rishi

Wa alaikumus salamu warahmatullah wabarakatuh.
Babu wani kaso da suke da shi, 
Sai dai zasu iya yin jinga a biya su kawai, tunda su ba Alkali bane.. Alkali ne gwamnati ke biya to bai ya anshi komai ba..
Shine Mai Ahlari yake nufi da ci da ceto.
Kuma shine Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:(DUK WANDA YA CETO GA DAN'UWAN SA, SAI DAN'UWAN NASA YA BASHI KYAUTA A CIKI SAI YA KARBA, TO YAZO MA WATA BABBAR KOFA DAGA CIKIN KOFOFIN RIBA).
Sunanu Abi dawud:3541.
Musnad na Imamu Ahmad:
Alkabir na Imamud Dabaraniy:
Daga Abu Umamah Al'bahiliy Allah ya Kara masa yarda.
Babin kyauta a wajen biyan bukata. Babi na 84 acikin kitabul Ijarah:17m.
Kamar Alkali ya kwato ma wani hakkin sa sai kuma a bashi wani abu ya ansa koda bai roka ba, ko rabon gado.
Haka protocol, yayi wa wani hanya sai ya bashi wani abu kuma ya karba, dadai sauransu.
Amma Wanda ba aikin sa bane da ake bayan sa a kai zai iya ansar na aikin sa.


Wallahu ta ala a'alam
Sheikh Shafiu Shehu Minna




https://www.google.com/search?q=%D8%A7%D9%84%D9%88%D8%AA%D8%B1+%D8%A8%D8%B9%D8%AF+%D8%A7%D9%84%D8%AC%D9%85%D8%B9+%D8%A8%D9%8A%D9%86+%D8%A7%D9%84%D8%B5%D9%84%D8%A7%D8%AA%D9%8A%D9%86&oq=%D8%A7%D9%84&aqs=chrome.1.69i57j69i59l3j69i61j69i60l2.2522j0j9&client=ms-android-transsion&sourceid=chrome-mobile&ie=UTF-8

No comments:

Post a Comment